MATEU ALEMANY YA AMSA TAMBAYAN KAN YIYUWAR CINIKIN FERRAN TORRES.
Daya daga cikin jigo a shugabancin Kungiyar kwallon kafa ta Fc Barcelona wato Mateu Alemany ya amsa tambaya kan yuwuwar kawo Ferran Torres na Manchester City.
Ana dade ana rade-radin Barca na zawarcin tauraron Manchester City gabanin kasuwar musayar 'yan wasa a watan Janairu tare da duba yiyuwan tattaunawa. Raunin ya shiga tsakani a kakar wasa ta bana, amma har yanzu Torres na cikin shirye-shiryen Pep Guardiola, kuma hakan na nufin Barca za ta biya wurin euro miliyan 50-60 don cimma yarjejeniyar.
Kamar yadda al'amura ke tafiya, hakan bana cikin tambaya ga Barcelona, wacce ke da kusanci da cika tsarin albashin La Liga da kuma bashi mai yawa. Hakan na nufin 'yan wasa ko ace wasu zasu tafi a watan Janairu kafin Barca ta cimma yarjejeniya, kuma hakan na iya nufin wasu kamar Philippe Coutinho za'a iya saka su kasuwa.
Amma idan Barca zata iya yin yarjejeniya, sun san abin da suke so suyi dakuma hanyar yin hakan.
Lokacin da aka tambaye shi game da Torres, jigo a Kungiyar ta Blaugrana Alemany ya gaya wa Sport cewa: "Muna da ra'ayoyi bayyanannu. Muna tafiya mataki-mataki".
Torres dan wasan gaban kasar Spain a yanzu yana da yarjejeniya a kungiyar Manchester City har zuwa shekarar 2025.
Comments
Post a Comment