YADDA GANAWA MAI DAUKAR HANKALI TA GUDANA TSAKANIN XAVI DA RAKITIC

Xavi kenan yayin da yake dago Rakitic daga faduwar da yayi a wasan Laligar jiya Sevilla vs Barca.


Koc din Barcelona Xavi yayi wasan duka da dan wasan tsakiya na Sevilla Rakitic, irin wasan nan na an dade ba a hadu ba, a haduwar Barcelona da Sevilla a daren Talata 21 ga December.

Kodayake daren na jiya Talata ba daren farin ciki ba ne ga Xavi kasancewar Sevilla ta riqe su diro 1-1 dukda da an bawa dan wasan sevilla Jules Kounde katin kora a minti na 64.

Dan wasan sevilla Papu Gomez shi ya fara cin Barca a minti na 32 da nufin qarawa qungiyarshi qarfi da take matakin ta 2 a gasar ta LaLiga.

Yayin da Ronald Araujo ya farke ana gab da tafiya hutun rabin lokaci.

Domin kallon labarin a faifan video danna link din nan

https://youtu.be/oU9HwKynWFM


Xavi ya taba buga wasa da Rakitic a shekararshi ta qarshe a matsayin dan wasa a Barcelona, a wata shekara mai cike da da farin tarihi,  shekarar "treble" wato shekarar da suka dauki LaLiga, Champions League da Copa Del Ray. Shekarar 2014-2015.

Rakitic, da ya bar Barcelona ya koma Sevilla a 2020, ya kife a qasa a gefen fili lokacin da Abde Ezzalzouli yayi mai fawul. Inda anan ne Xavi ya dagoshi ya rungumeshi cikin mutuntaka da kulawa.



Wannan abu ya qayatar sosai, domin ganin video din yadda abubuwan suka gudana cikin harshen Hausa, tuntubi FCB Golden TV a YouTube.



Abin ya faru ne Koc Xavi yana tsaye cikin aikinshi na koc, sbd haka yana ganin dan wasan dan shekara 33 Rakitic a qasa, bai duba cewa ya taimakawa Sevilla wajen zura musu qwallo ba, kawai sai yai maza yaje gareshi ya miqa mishi hannu ya dagoshi cikin dariya yana mai dukanshi a gadon baya, Rakitic yana dariya shima ya miqe, bayan da ya miqe ne suka kalli juna sukayi rungumar yaushe rabo, inda zabi ya qara bashi tap da hannu a gadon baya.

Comments