Posts

Showing posts from January, 2022

AN KAMA MASON GREENWOOD BISA ZARGIN FYADE DA CIN ZARAFI

Image
An kama Mason Greenwood bisa zargin aikata fyade da cin zarafi a yau lahadi, biyo bayan wani faifayin hotuna da budurwarsa Harriet Robson ta wallafa a shafukan sada zumunta. A cikin Hotunan, an saka jerin hotunan jikinta da aka yi wa dukan tsiya a cikin story ta na Instagram, yayin da kuma aka raba wani faifan sauti. Sanarwar da ‘yan sandan Greater Manchester ta fitar a yammacin yau, inda ta tabbatar da cewa an tsare dan wasan na Manchester United yayin da ‘yan sanda ke binciken lamarin. SANARWAN MANCHESTER UNITED AKAN GREENWOOD Kulub din dan wasan ya kuma fitar da wata sanarwa, inda ya bayyana cewa an cire shi daga dukkan ayyukan kungiyar ta farko. An fitar da wannan bayani ne kafin a tabbatar da kama shi da rundunar ‘yan sandan yankin tayi.  "Mason Greenwood ba zai koma atisaye ko buga wasa ba har sai an samu sanarwa," inji Manchester United kan lamarin.

KOKUN SAN MAIKE FARUWA FILIN ATTISAYEN BARCELONA

Image
  Yusuf Demir ya dawo atisaye a Barcelona ranar Talata kafin wasan da za su kara da Linares Deportivo a gasar Copa del Rey ranar Laraba da  misalin  karfe  7:30 na dare Dan wasan na Austriya, wanda Yazo fc Barcelona  a matakin aro daga kungiyar Rapid Vienna, baya cikin shirin koci xavi Hernandez kuma an ba shi hutu don gwada sabuwar kungiya a wannan watan. Duk da haka yayin da ake jiran yanke shawara kan makomarsa, ya koma horo yayin da Barça ke shirin shiga gasar cin kofin Sarkin sarakuna  na bana. Wato king Cup Sun yi atisaye ba tare da 'yan wasa takwas da suka gwada  Covid-19 ba suke dauke  da Cutar ba ,na baya-bayan nan wanda suka  gwada  su biyu ne  su ne Pedri da Ferran Torres, don haka Xavi Hernandez     ya yi amfani da yan wasan kungiyar B da yawa don daidaita lamuran. Memphis Depay da Ansu Fati suma sun halarci cikakken atisayen dukdahaka amma Xavi ya ce   wasan   Linares ya zo mu...