AN KAMA MASON GREENWOOD BISA ZARGIN FYADE DA CIN ZARAFI

An kama Mason Greenwood bisa zargin aikata fyade da cin zarafi a yau lahadi, biyo bayan wani faifayin hotuna da budurwarsa Harriet Robson ta wallafa a shafukan sada zumunta. A cikin Hotunan, an saka jerin hotunan jikinta da aka yi wa dukan tsiya a cikin story ta na Instagram, yayin da kuma aka raba wani faifan sauti. Sanarwar da ‘yan sandan Greater Manchester ta fitar a yammacin yau, inda ta tabbatar da cewa an tsare dan wasan na Manchester United yayin da ‘yan sanda ke binciken lamarin. SANARWAN MANCHESTER UNITED AKAN GREENWOOD Kulub din dan wasan ya kuma fitar da wata sanarwa, inda ya bayyana cewa an cire shi daga dukkan ayyukan kungiyar ta farko. An fitar da wannan bayani ne kafin a tabbatar da kama shi da rundunar ‘yan sandan yankin tayi. "Mason Greenwood ba zai koma atisaye ko buga wasa ba har sai an samu sanarwa," inji Manchester United kan lamarin.